Rundunar yan sandan jihar Legas ta tabbatar da korar wani jami’inta bisa zargin satar jariri.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar yan sanda ya bayyana Banjemi Hundyin a ranar Alhamis.

Ya ce ana zargin jami’in su mai suna Ukpabio bisa tilastawa wata da kwace mata jariri.

Ukpabio ya fadawa mahaiifiyar jariri cewa dole ta bashi yaron kuma idan taki zai kwace sauran yayanta.

Sannan bayan karbar jariri ya siyar da shi akan naira miliyan uku.

Sannan ya bai wa mahaifiyar naira dubu 185.

Sai dai bayan tabbatar da bincike rundanar yan sandan jihar Legas ta kori Ukpabio bayan aikata laifin a cewar Banjemin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: