Majalisar wakilai a Najeriya ta dakatar da babban bankin Najeriya CBN a kan don hana bankin yan kasuwa karɓar bayanan kafofin sada zumunta na abokan hulɗar su.

Hakna ya biyo bayan kudirin shugaban marasa rinjaye a majalisar Hon. Kingsley Chinda da wasu yan majalisa tara da su ka goyi baya.


A zaman da majalisar ta yi a yau sun amince tare da umartar babban bankin Najeriya CBN da ya dakatar da bankunan yan kasuwa wajen karbar bayanan kafofin sa da zumuntarsu.
A bayanin kudirin da yan majalisar su ka gabatar, sun ce bayanan kafofin sa da zumunta na abokan huldar ba zai amfanar da komai ba.
Ko a baya sai da aka bayyana haka a matsayin rashin tsaro tare da watsi da haka.
Waɗanda su ka kai kudirin sun ce neman bayanan zai sanya ƴan kasar cikin mawuyacin hali, musamman ga mutanen marasa ilimi da matsakaita.
Daga karshe majalisar ta amince da kudirin tare da umartar babban bankin da ya dakatar da neman bayanan a kai.