Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da wasika majalisar wakilai ta kasa don amincewar raba naira biliyan 500 ga ƴan kasar.

Wasikar da shugaban ya aikewa majalisar wakilai wadda shugaban majalisar Tajudden Abbas ya karanta a zaman majalisar na yau.
Wasikar ta ce wajibi ne a samar da hanyar da za a ragewa yan kasar radadin cire tallafin man fetur.

Wasikar ta bukacin yan majalisar da su amince da buƙatar don tallafawa yan kasar sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi.

Bayan kammala karanta wasikar, shugaban majalisar ya ce za su fara duba yuwuwar hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Tun a shekarar 2022 aka samar da tsarin bayar da tallafin ga yan Najeriya bisa cire tallafin man fetur da aka shirya yi tun a shekarar.