Dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, zai fuskanci tuhumar mallakar bindiga da harsashi ba bisa ƙa’ida ba.

rahoton da jaridar The Nation ya tabbatar da cewa za a gurfanar da Emefiele a gaban kotu a birnin Legas a sati mai zuwa kan zargin mallakar makamin ba bisa ƙa’ida ba.

Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) a ranar Alhamis tace ta kai Emefiele kotu, amma ba ta yi bayani ba kan tuhumar da ta ke yi masa ba.

Sai dai, wata babbar kotun tarayya mai zamanta a Apo, birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a ta yi hukunci cewa kama Emefiele da tsare shi da ake yi ya saɓawa doka.

Hakan na zuwa ne dai bayan wata babbar kotu mai zama a Maitama a birnin tarayya Abuja, ta umarci DSS ta kai Emefiele kotu ko ta sake shi cikin sati ɗaya.

Emefiele, a cewar majiyoyi zai fuskanci tuhuma biyu kan mallakar bindiga ba tare da lasisi ba, wanda hakan ya saɓawa sashi na 4 na dokar mallakar makami na shekarar 2004 wanda ya cancanci hukunci a sashi na 27 (1) (b) (i) na dokar.

Ana kuma zargin dakataccen gwamnan babban bankin da mallakar alburusai 123 ba tare da lasisi ba.

Emefiele ya aikata laifukan ne dai a adireshin No.3B Iru Close, Ikoyi, Legas, a ranar 15 ga watan Yunin 2023.

An kama Emefiele ne dai a ranar 10 ga watan Yuni, kwana ɗaya bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da shi daga muƙaminsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: