Gwamnatin Najeriya ta janye jami’an da ke kula da wasu mutane a Najeriya ciki har da wasu tsofaffin gwamnonin Kasar.

Jaridar Punch ta rawaito cewa shugaban ‘yan sanda na Kasa Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin janye masu gadin tsohon Sakataren gwamnatin tarayya da tsofaffin Ministoci.

Umarnin janye jami’an ya shafi wadanda su ka taba zama ‘yan majalisar tarayya da kuma uwargidan tsohon shugaban Kasa Aisha Buhari da wani dan uwanta.

Wasikar janyewar da aka aikawa Hedikwatar yan sandan kwantar da tarzoma Mopol ta 45 a birnin tarayya Abuja ta zayyano sunayen tsofaffin Gwamnonin da suka hada da tsohon gwamnan Gombe, Bauchi, Imo Ogun da kuma Zamfara, sai tsohon Ministan harkokin ‘yan sanda da tsohon Ministan Neja-Delta da Halliru Jika.

Sauran sun hada da tsofaffin Ministoci na ma’adanai, kimiyya da fasaha da ayyukan wutar lantarki da kuma na kasafin kudi.

Umarnin na Kayode ya hada da tsohon shugaban PDP na kasa Iyorchia Ayu da kuma shugabar matan jam’iyyar APC.

Wasikar da aka fitar a makon da muke ciki ta bayyana cewa wajibi ne ayi gaggawar aiwatar da umarnin da aka bayar nan take.

Leave a Reply

%d bloggers like this: