Rahotanni na nuni da cewa shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Sanata Abdullahi Adamu yayi murabus daga kan mukaminsa na shugaban Jam’iyyar.

Jaridar Daily Trust ita ce ta tababtar da hakan a ranar Litinin.
Adamu wanda ya aike da wasikar murabus din zuwa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa Femi Gbajabiamila a yammacin ranar Lahadi.

Sanata Adamu wanda ya zama shugaban jam’iyyar ta APC a watan Maris din shekarar 2022 da ta gabata kuma ya yi murabus din ne a lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke halartar taron kungiyar AU a Kasar Kenya.

Murabus din Adamu na zuwa ne a lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da taron majalisar kolin Kasar wato NEC a makon da muke ciki.
Wani makusanci ga tsohon shugaban jam’iyyar ya shaidawa Daily trust cewa Adamu ya sauka daga mukamin ne sakamakon shirin tsige shi da aka yi a taron ƙolin jam’iyyar da za a gudanar a ranar Talata da Laraba mai zuwa.
Ya kara da cewa bayan samun labarin wasu makusantan shugaban ƙasa guda biyu na shirin tattara sa hannun mahalarta taron domin amincewa da tsige shi,wanda hakan ya sanya yayi murabus din.
Ba tun yanzu ba aka samun rashin jituwa da Sanata Abdullahi Adamu bayan ya goyi bayan tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawal a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ta APC.
Bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi nasara a zaben su ka ci gaba da samun rashin jituwa a tsakaninsu.
Koda a baya bayannan sai da suka samu sabani akan shugabancin wakilan jam’iyyar a Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.