Gwamnatin Jihar Taraba ta kafa wani kwamiti da zai yi aikin bincikowa tare da kwato kadaron gwamnatin Jihar a faɗin Najeriya.

 

Sakataren gwamnatin Jihar Gebon Kataps shine ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi.

 

Sakataren ya ce an dorawa kwamitin alhakin gano kadarorin Jihar a Jihar Kaduna da ofishin Jihar ta Taraba da ke Jihar Legas da kuma birnin tarayya Abuja.

 

Gebon ya kara da cewa an kuma dorawa kwamitin nauyin gano dukkan inda kowacce irin kadarar gwamnatin Jihar ta ke a faɗin Najeriya.

 

Sakataren ya ce bayan gano kadarorin kwamitin zai kuma fadi kudin kowace kadara tare da mikawa gwamnatin jihar.

 

Gebon ya bayyana cewa kwamitin zai kammala binciken sa ne nan da makwanni hudu masu Zuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: