Majalisar Sarakunan Arewa da ke Kudancin Najeriya ta koka kan tsare shugabanta Sarkin Hausawan Jihar Legas Alhaji Aminu Yaro da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar da Majalisar ta fitar ta hannun Jarman Legas Yarima Shettima a ranar Litinin.
Majalisar ta bayyana cewa kuskure ne hukumar ta DSS ta kama Sarkin na hausawa da kuma matarsa har tsawon kwanaki uku ba tare da gurfanar da su ba a gaban Kotu.

Sanarwar ta kara da cewa duk da Sarkin na Hausawan abokin dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya ne Godwin Emefiele ne hakan da DSS ta yi ya zubar masa da alfarma tare da cin zarafi dukkan al’ummar Hausawa mazauna kudancin Najeriya.

Wata majiyar ta shaidawa Daily Trust cewa hukumar ta gayyaci Sarkin Hausawan ne tare da matarsa akan tuhume-tuhumen da ake yiwa Emefiele dakataccen Gwamnan Babban Bankin Kasa.
Amma mai magana da yawun hukumar ta DSS Peter Afunanya ya shaidawa na Daily trust cewa ba zai iya cewa komai ba akan batun.