Hukumar kashe gobara ta ƙasa reshen jihar Kano ta ce wasu shaguna sun kone a sakamakon wata gobara da ta kama a kasuwar Rimi.

Al’amarin ya faru a daren ranar Laraba wayewar yau Alhamis.
Mai magnaa da yawun hukumar Saminu Yusif Abdullahi ya ce shaguna goma ne su ka kone a sakamakon gobarar.

Ya ce wani mai suna Magaji Umar ne ya sanar da su tashin gobarar.

Ya ce gobarar ta faru a ɓangaren siyar da tabarmi, gado da kayan katako.
Jami’an kashe gobarar sun bazama don ganin an daƙile haka.
Sai dai shaguna goma sun kone da kaya a ciki.
Ya ce a cikin wurin da su ka kone akwai shaguna shida da rumfuna huɗu.
Hukumar ta gano cewa gobarar ta faru ne sakamakon wutar lantarki.
