Hukumar FIRS mai alhakin tara haraji a Najeriya, ta shaida cewa daga watan Junairu zuwa karshen watan Yunin 2023, ta samu Naira tiriliyan 5.5.

 

A tarihin Najeriya, an ruwaito cewa ba a taba yin lokacin da aka samu wadannan kudin shiga ba.

 

Shugaban FIRS na kasa, Muhammad Nami ya shaida haka a lokacin da yake gabatar da jawabi a kan kudin da ake sa ran samu daga haraji a 2023-2024.

 

Muhammad Nami ya yi magana a gaban majalisar tattalin arziki ta kasa watau NEC a taron da aka yi na ranar 20 ga watan Yulin 2023 a fadar Aso Rock.

 

Jawabin shugaban hukumar yana kunshe da bayanin kudin shigan da ya shigo asusun Najeriya a bana, ya ce FIRS ta cin ma sama da 100% na burinta.

 

Rahoton ya ce abin da aka yi lissafin gwamnatin Najeriya za ta samu daga watan Junairu zuwa karshen Yuni naira tiriliyan 5.3 za a iya zarce hakan da Naira biliyan 200.

 

A cikin watanni shida na farkon shekarar nan, an tara Naira Tiriliyan 2.03 daga saida mai, wanda hakan bai kai Naira Tiriliyan 2.3 da aka ci burin samu ba.

 

Alhaji Nami ya ce harajin da su ka fito daga bangaren da ba na mai ba ya zarce Naira tiriliyan 2.98 da ake hari, sai da FIRS ta iya tatso Naira Tiriliyan 3.76.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: