Majalisar tattalin arziƙi ta ƙasa (NEC) karkashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ta umarci hukumar bada agajin gaggawa ta gaggauta fito da hatsi.

 

NEC ta umarci hukumar NEMA ta raba wa jihohin Najeriya hatsin cikin mako ɗaya ko biyu masu zuwa domin sauko da farashin kayan binci a faɗin ƙasar nan.

 

Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammed ne ya bayyana haka yayin da yake hira da ‘yan jarida dangane da abinda suka tattauna a taron NEC ranar Alhamis, 20 ga watan Yuli.

 

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ya jagoranci taron wanda ya gudana a fadar Aso Rock da ke birnin tarayya Abuja.

 

Kauran Bauchi ya ce Shettima ya umarci NEMA ta gaggauta buɗe rumbunan gwamnati, ta fito da hatsi kuma a cewarsa za a haɗa hannu da jihohi domin sakon ya isa ga talakawa.

 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamna Muhammad na nuna damuwa kan tsadar abinci, a cewarsa batun abinci ne babban abinda majalisar NEC ta maida hankali a zaman.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: