Hedikwatar tsaro ta ce rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji da dama a yankuna uku na kasar.

Daraktan yada labarai na rundunar tsaron, Manjo Janar Edward Buba shi ya bayyana haka a ranar Alhamis 20 ga watan Yuli a Abuja.


Ya ce sun samu nasarar ne a cikin makwanni biyu a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma da kuma Arewa maso Gabas, inda ya ce rundunar ta yi luguden wuta ta sama da kasa.
Ya kara da cewa a Arewa maso Gabas rundunar sojin ‘Operation Hadin Kai’ ta hallaka ’yan ta’adda da dama da kama masu ba su bayanan sirri a kananan hukumomin Mafa da Kukawa da kuma Konduga.
Ya tabbatar da cewa ‘yan ta’adda da dama sun mika wuya bayan sun sha luguden wuta ta sama da kasa inda suka tabbatar musu cewa su fa sun gaji da wannan akidar tasu.
Buba ya ce a Arewa ta Tsakiya, sundunar ta kai samame maboyar ‘yan bindiga tare da kwato muggan makamai a kananan hukumomin Mangu da kuma Jos ta Kudu a jihar Plateau.
Sannan rundunar ta kai samame maboyar masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Obi ta jihar Nasarawa da kuma karamar hukumar Wukari a jihar Taraba.
Yayin da a Arewa maso Yamma, kakakin hedikwatar tsaron ya bayyana rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ ta kai samame a maboyar ‘yan fashin daji a kauyuka da dama a kananan hukumomi daban-daban.
Ya ce rundunar ta yi luguden wuta ta sama akan ‘yan bindigan tare da hallaka wasu a kananan hukumomin Batsari da Tangaza da kuma Maru da ke jihohin Katsina da Sokoto da kuma Zamfara.
