Ƙungiyar ƙadago a Najeriya ta sanar da yunƙurin shiga yajin aiki da za ta fara daga ranar 2 ga watan Agusta mai kamawa.

Ƙungiyar ta ce ba za ta ci gaba da zuba ido al’ummar ƙasar na cigaba da shan wahala bat un bayan da aka cire tallafin man fetur.


Ma’ajin ƙungiyar na ƙasa Hakeem Ambali ya tabbatar da matakin yajin aikin da za su yin a ƙasa baki ɗaya wanda y ace sun bai wa gwamnatin tarayya mako guda don tabbatar da cika alƙawuran da ta ɗauka.
A baya ƙungiyar ta shirya tafiya yajin aiki sai dai sun dakatar bayan tattaunawa da ɓangaren gwamnatin tarayya.
Daga cikin matsayar da aka cimma akwai ƙarin albashi ga ma’aikata da sauran alƙawuran da gwamnati ta yi don rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Haka kuma gwamnatin tarayya ta shiugar da ƙungiyar ƙara a kotu sannan kotun ta dakatar da ƙungiyar daga shiga yajin aikin.
Majiya mai ƙarfi ta shaida cewar ƙungiyar ta ɗayuki matakin hakan ne bayan da aka samu tsaiko daga yarjejeniyar da aka yi da gwamnati a zaman da su ka yi a baya.