Rahotanni na nuni da cewar ana cigaba da samun mutanen da ke mutuwa sakamakon cizon maciji a Najeriya.

 

Wani bincike da aka gudanar a cibiyar kula da mutanen da macijin ya ciza a jihohin Filato, Gombe, ya nuna ƙaruwar mutanen da ke mutuwa a kai.

Mutanen da su ka fi fadawa hatsarin manoma da su ke yin arangama da hi a cikin gona idan su na aiki.

 

Haka kuma fatake naa daga cikin mutanen da hakan ke rutsawa da su.

Sai dai mutanen na mutuwa a asibitoci musammna bangaren kwararru don kula da mutanen da macijin ya ciza daa kuma wadanda su ke a wajen masu maganin gargajiya.

 

Dakta Abubakar Ballah shugaban asibitin Kaltungo da ke kula da mutanen da maciji ya ciza ya ce a kowacce rana su na karɓar sabbin mutane 11 masu larurar.

Haka abin yake a asibtin Zamko na jami’ar Jos da kuma na Karim Lamido a jihar Taraba wanda su ka bayyana karuwar mutanen.

 

Hukumomi na kira ga gwamnatin tarayya ta da mayar da hankali wajen samar da maganin cizon maciji na gida domin rage yawan mutanen da ke mutuwa a koda yaushe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: