Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce sun samu damar magance matsaloli da dama a zaɓen shekarar 2023 da ya gabata.

 

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu ne ya bayyana haka a jihar Legas, yayin taron masu ruwa da tsaki don duba zaɓen da ya gabata.

 

Ya ce babu wani abu da hukumar ta boye kamar yadda wasu mutane ke zargi.

 

Ya kara da cewa akwai matakai da dama da hukumar ta dauka tare da magance matsaloli masu yawa gabanin zaben da ya gabata.

 

Sannan a ya ce hukumar za ta cigaba da yin iya kokarinta don ganin an cigaba da kawo sabbin abubuwa na cigaba da za su taimakawa hukumar.

 

An gudanar da taron yau a jihar Legas tare da duba ayyukan da aka gabatar a zabukan shekarar 2023 da mu ke ciki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: