Ƙungiyar kwadago a Najeriya ta tabbatar da janye yajin aikin da ta fara a jiya Laraba.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa Joe Ajaero ne ya tabbatar da haka yau bayan zama majalisar zartarwa na kungiyar da ya gudana.
Hakan ya biyo bayan shiga tsakani da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a jiya Laraba.

Shugaban ya gana da shugabannin ƙungiyar kwadago da ƴan kasuwa a yammacin Laraba.

Ma’ajin kungiyar na ƙasa Hakeem Ambali ya tabbatarwa da wakilin karidaar Punch cewar sun janye yajin aikin bayan shiga tsakani da majalisar dokoki ta kasa ta yi da kuma ganawar da su ka yi da shugaban kasa a jiya Laraba.
Ƙungiyar ta ce ta janye yajin aikin ne sakamakon mayar da hankali da gwamnati ta yi dangane da bukatunsu.
Masu zanga-zanga a jiya sun kutsa cikin maajalisar dokoki ta kasa, yayin da sauran jihohi ma su ka gudanar da tasu zanga-zangar don nuna damuwa bisa tsadar mna fetur wanda hakaan ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a kasa.