Shugabannin jam’iyyar APC na Jihohi 36 a Najeriya sun goyi bayan tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje na zama shugaban jam’iyyar na kasa.

Shugabannin sun kaiwa Ganduje ziyarar goyon bayansa a Abuja awanni kafin tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyya.
Ƙungiyar shugabannin APC na jihohin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Ali Bukar Dalori, wandaa ke shugabantar jamiyyar a Borno tare da wasu ƙungiyoyin da su ka marawa Ganduje baya ƙarƙashin jagorancin babbna daraktan Injiniya Kailani Muhammad.

A yayin ziyarar sun tabbatar da goyon bayansu ga Dakta Abdullahi Ganduje.

Su ka ce a shirye su ke domin yin aiki da shi, sannan sun je tare da tayashi murna domin samun tabbacinsu na zamansa shugaba.
Dakta Ganduje ya ce akwai buƙatar saka fasahar zamani a cikin tafiyar jam’iyyar.
Shi ma daraktan gamayyar kungiyoyin da su ka mara baya Injiniya Kailani, ta ce “Mun gamsu da salon shugabancinka, a matsayin wanda ya ciyar da Kano gaba ta fuskar tattalin arziki, mu na rokonka da ka tafiyar da jam’iyyar a haka”.
Ganduje ya fahimci yadda ake samun matsaala daga shugabannin jam’iyyar wand aya alakanta hakan da rashin kyakkyawar mu’amala da sauran ƴan jam’iyya.
A yau ake sa ran tabbaatar da Dakta Abdullahi Ganduje matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa, bayan da tsohon shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu ya ajiye aiki.