Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar lalata maɓoyar ƴan bindiga tare da wasu da dama a jihohin Katsina da Sokoto.

Jami’an sunƙato makamai da dama daga wajen yan bindiga.
Rundunar Operation Hadarin Daji sun samu narar ne a ranar 3 ga watan Agusta da mu ke ciki yayin da su ka kai hari ƙaramar hukumar Isa a jihar Sokoto.

Haka kuma runduna ta Takwas sun shiga Sabon Birni sannan su ka kusta dazukan Kusabunni, Tafkin Gawo, Alumdawa, Unguwar Mailete da Malamawa a nan ma su ka kora ƴan bindgan da ke wajen.

A jihar Katsina kuwa an samu nasarar kai hari garin Kore da ke ƙaramar hukumar Ɓatagarawa a nan ma su ka kuɓutar da wasu da aka yi garkuwa da su.
Mutane huɗu jami’an su ka yi nasarar kuɓutarwa waɗanda aka yi garkuywa da su a Unguwan Magudu da ke ƙaramar hukumar Ɗandume a jihar Katsina.
Jami’an sun samu nasarar ƙato makamai daga wajen ƴan bindigan tare da hallaka wasu yayin da aka kuɓutar da dabbobi da ake zargi masu garkwuan sun sace.
