Kungiyar dillalan mai ta kasa IPMAN ta bayyana cewa za a iya samun karin kudin man fetur a kasa Najeriya har zuwa naira 750.

kungiyar ta bayyana haka ne tare da cewa hakan ya sami asaline da tashin dala da aka samu a kasar Najeriya.
Ta ce yanzu haka Dala ta kai sama da naira 900 a kasar don haka dole ne man fetur ya kara kudi a kasar.

Haka kuma Najeriya a wannan halin ba ta fara tace man fetur da ta yi alkawarin za ta fara ba.

Ƙungoyar ta ce hakan zai faru ne sanadin amfani da dalar amuruka wajen siyo tataccen man fetur.
Farashin man fetur ya yi tashiin gwauron zabi tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rashin cigaba da biyan tallafin man fetur a yayin jawabinsa jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya.