Akalla sojojin Najeriya 20 ne su ka rasa rayukansu a wani harin kwanton bauna da ‘yan bindiga suka kai musu a wani daji da ke kan hanyar Zungeru zuwa Tegina a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Lahadin da ta gabata.
Wata majiya mai ƙarfi ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da sojojin ke kan hanyarsu ta zuwa wasu kauyuka da ‘yan bindigar suka mamaye a cikin karamar hukumar Wushishi ta Jihar.

Majiyar ta bayyana cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ne dai ‘yan bindigar suka kai hari kauyukan na wanda hakan ya sanya al’ummar yankin tsere zuwa garuruwan Zungeru da Wushishi.

Rundunar soji ta bayyana cewa mutane 18 da aka hallaka jami’an rundunar sojin kasa ne yayin da biyu daga cikinsu kuma na sojin sama ne.
Channels TV ta rawaito cewa sojoji 13 ne aka hallaka a ranar Lahadi, yayin da aka sake hallaka Takwas cikin harda wani Kaftin daya da Manjo daya a harin kwanton ɓauna da aka kai musu a ranar Litinin.
