Rundunar yan sanda a jihar Katsina ta samu nasarar hallaka wwani ɗan bindiga tare da ƙwato bindiga ƙirar AK47.

Kakakin ƴan sanda a jihar ASP Abubakar Sadiƙ ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Sanarwar ta ce an hallaka ɗan bindigan ne yayin da jami’ansu su ka yi ƙoƙarin daƙile wanii hari a ƙauyen Korogo da ke ƙaramar hukumar Jibia a jihar.

Ya ƙara da cewa sun samu nasarar ƙwato harsashi sama da 100 daga wajen ƴan bindigan.

Ya ce a farkon daren ranar Talata ne su ka samu bayanai a cewa ƴan bindiga sun shiga ƙauyen da muggan makamai sannan sun fara harbin iska.

Tuni baturen yan sanda da ke Jibia ya haɗa kan jami’ansa domin daƙile harin.

Kuma sun ɗakko gawar ɗan bindigan da su ka hallaka tare da kuɓutar da dabbobi guda sittin da bindiga ƙirar AK47 da kuma harsahsi mai yawa.

ASP Abubakar Sadiƙ ya ce hukumar na ci gaba da bincike a kan lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: