Gwamnatin Jihar Gombe ta kaddamar da rabon tallafin kayan abinci a Jihar domin ragewa mazauna Jihar radadin kuncin rayuwa da ake ciki a Kasar bayan cire tallafin man fetur.

Gwmnan Jihar Muhammad Inuwa Yahya ne ya kaddamar da rabon a garin Dadin Kowa da ke cikin Karamar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa kaddamar da rabon kayan tallafin gwamnatin ta yi hakan ne domin tallafawa sama da mutane 450,000 a kananan hukumomi 11 da ke fadin Jihar.

Yahya ya kara da cewa bayan kaddamar da tallafin an fara da bai’wa mutune dubu naira 30,000, inda kowane mutum zai samu shinkafa mai nauyin Kilo biyar da kwalin Taliya daya da buhunhunan taki biyu da lita biyu na maganin kashe kwari.

Inuwa Yahya ya bayyana cewa an saka tallafin kayan noma a cikin rabon kayan abincin ne ganin yadda al’ummar Jihar suka dogara da noma cikin rayuwarsu.
Gwamna Inuwa ya ce bayar da tallafin noman zai taimaka matuka wajen samar da isassun kayan abinci a lokacin rani.
Yahya ya ce za a bayar da tallafin ne bayan kalubalen da magidanta ke ciki a Jihar sakamakon tabarbarewar tattalin arziki a Kasa.
Sannan yayi kira ga masu hali da su taimkawa talakawa domin fitar da su daga cikin halin kuncin da suke ciki.