Wasu masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da wata matar faston cocin Redeemed Christian Church of God a Jihar Kwara.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 8:45 na daren ranar Alhamis a shagonta.
‘Ƴan bindigar sun sace matar faston ne a kauyen Elerinjare da ke karamar hukumar Ifelodun ta Jihar.

Matar faston mai suna Mrs Blessing Ajiboye an yi garkuwa da ita ne tare da masu taimaka mata su biyu a shagonta.

Sai dai daga bisani an sako masu taimaka mata bayan an yi garkuwa da su.
Fasto mai suna Johnson Olalekan Ajiboye ya bayyana cewa biyu daga cikin yan bindigar da suka yi garkuwa da matar tasa mata.
Faston ya ce maharan sun shiga kauyen ne ta cikin wani daji da ke bayan makarantar firamaren kauyen.
Ya kara da cewa maharan sun yi garkuwa da matar tasa ne bayan ya fita daga shagon domin dauko wani abu a gida.
Limamin cocin ya ce ‘yan bindigar basu dauki komai ba a cikin shagon kawai sun sace matar ne bayan sun ajiye jaririn ta.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ya ce bashi da cikakken bayani game da faruwar lamarin.