Hukumomi a ƙasar Burtaniya sun zargi tsohuwar ministar albarkatun man fetur a Najeriya Diezani Alison Madueke da bayar da kwangiloli don karɓar cin hanci.

An kama Diezani ne dai tun a watan Oktoban shekarar 2015 kan zargin cin hanci wanda daga bisani aka bayar da belinta.

Ƴan sanda a Burtaniya sun zargeta ne da bayar da kwangilolin man fetur da iskar gas domin karɓar cin hanci, wanda ta karɓi fan din Ingila mai yawa.

Hukumar yaƙi da cin hanci ta duniya ta ce tuhumar da ake yi wa tsohuwar ministar an yi ne bayan zurfafa bincike a kai.

Ko a bara sai dai sai da hukumar yaƙi da yiwa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta ƙace wasu kuɗaɗe daga hannuntatare da wasu kadarori.

Hukumar yaƙi da cin hanci ta duniya ta ce ta samu Diezani da laifin karɓar na goro ta hanyar bayar da kwangilolin man fetur da iskar gas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: