Gwamnan jihar Kaduna Alhaji Uba Sani ya bayyana aniyar gwamnatinsa na ɗaukar matasa 7,000 aikin tsaro na sa kai domin taimakawa jami’an soji a jihar.

Alhaji Uba Sani ya bayyana haka ne a yayin ganawa da gidan talabiji na Channel ta cikin shirinsu na Politics Today.
Gwamnan wanda ya gana da manyan hafsoshin tsaro, ya basu tabbacin goyon bayansa daga dukkan abinda su ka buƙata a gwamnatinsa.

Ya ce a watanni ukun mulkinsa, sun aiwatar da abubuwa masu tarin yawa wanda ya shafi matsalar rashin tsaro a Kaduna.

Kuma shi ne gwamna na farko da ya fara ganawa da manyan hafsoshin tsaron Najeriya tare da babban hafsan tsaron ƙasa wanda ɗan jihar Kaduna ne.
Cikin ganawar da su ka sun fahimci juna tare da duba hanyoyin da za a kawo ƙarshen matsalar tsaro da ake fama a jihar.
Daga cikin abubuwan da ya gano cikin tattaunawarsu, ya ce ya fahimci jami’an soji na buƙatar taimako.
A don haka ya yanke shawarar ɗaukar matasa 7,000 domin shiga aikin tsaro na sa kai yadda za a taimakawa jami’an tsaron.