Tohon ɗantakar shugaban ƙasa Peter Obi da jam’iyyar daya yi wa takara ta Labor Party sun musanta batun haɗaka da jam’iyyun NNPP da PDP.

An dai hango wasu hotuna da ke yawo wanda aka ga tsaffin ƴan takarar shugabanƙasa na jam’iyyun PDP Atibu Abubakar da NNPP Rabi’u Kwankwaso da kuma na jam’iyyar LP Peter Obi na tattaunawa.
Kakakin jam’iyyar Labor Party Dakta Tanko Yunusa ne ya musanta batun haɗewar jam’iyyun wanda ya ce ko da hakan za ta kasance sai dai su zamto cikin ƙarƙashin jam’iyyarsu.

Ya ƙara da cewa ƴan takarar na tattaunawa ne domin samar da fahimta a tsakaninsu amma ba batun haɗewa don dunƙulewa tare da zama jam’iyya ɗaya ba.

Ya ce tattaunawar da ƴan takarar su ka yi ba ta da alaƙa da batun haɗewa wajen guda a halin da ake ciki.
Jam’iyyun NNPP da PDP da kuma LP sun na daga cikin waɗanda su ka samu ƙuri’a mafi rinjaye a zaɓen shugaban ƙasa da aka yin a shekarar da mu ke ciki.