Rundunar sojin saman Najeriya ta sha alwashin kulawa da rayuwar iyalan sojojin da su ka yi hatsari a jihar Neja.

Babban hafsan sojin saman Najeriya Air Marshal Hassan Abubakar shi ne ya bayyana haka kamar yadda hakan ke ƙunshe cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar Edward Gabkwet ya sanyawa hannu.
Sanarwar ta ce rundunar ba za ta manta da iyalan waɗanda su ka rasa ransu a hatarin jirgin ba duba ga gudunmawar da su ka bayar.

Haka kuma rundunar za ta cigaba da tunawa da sojojin da suka mutu ganin yadda su ka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimtawa ƙasar.

Haka kuma babban hafsan sojin saman zai gana da sashen mutanen da su ka yi hatsarin jirgin.
A makon da ya gabata ne wani jirgin samar sojin Najeriya ya yi hatsari wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa rayuwar sojoji da dama.