Ministan birnin tarayya Abuja a Najeriya Nyesom Wike ya haramta talla da kasuwanci a bakin titunan birnin Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan da ministan ya bayar da izinin rushe wasu gidaje masu yawan gaske a birnin Abuja.

Wike ya bayyana cewar ya haramta talla da siyar da kayyaki a bakin titi ne bisa barazanar tsaro da birnin ke fuskanta.

Ya ce ya fahimci Abuja na fuskantar duhu saboda rashin fitulu da za su haska birnin, kuma zai tabbatar komai ya koma daidaita yadda za a cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali.

Sannan ya ce ba zai lamunci samar da haramtattun tashoshin bakin titi a Abuja ba, kuma ya hori masu alhakin kula da hakan da su gaggauta samar da makoma.

Haka kuma ya ce za su duba dukkanin masu kasuwanci musamman gidajen abinci da aka yi ba bisa ƙa’ida ba kuma za a ɗauki matakin tashinsu muddin an yi a wuraren da ba su dace ba.

Kalaman ministan dai sun fara ɗaukar hankali tun bayan rantsar da shi wanda ya lashi takobin rushe dukkan gine-gine da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: