Gwamnatin ƙasar Burtaniya ta buƙaci a gaggauta sakin hamɓararren shugaban ƙasar Nijar Mohammed Bazoum.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitara yau Laraba, ta yi Alla-wadai da cigaba da tsare Mohammed Bazoum wanda ta ayyana hakan a matsayin abin day a saɓawa doka.

Gwamnatin Burtaniya ta cigaba da nuna goyon bayanta ga ƙungiyar ECOWAS bisa ƙoƙarin da ta ke na dawo da mukin demokaraɗiyya a ƙasar.

Sannan ta yi kira da kakkausar murya da a gaggauta sakin Mohammed Bazoum da iyalansa da kuma wasu daga cikin masu dafa masa a gwamnati.

Ministan jami’an tsaron ƙasar Burtaniya na gab da ganawa da manyan harsishin tsaron Najeriya da kuma shugabannin sojin ƙasar dangane da juyin mukin da aka yi a jamhuriyar Nijar.

Sanarwar ta ce ƙasar Burtaniya da Najeriya na da alaƙa mai tsawo wanda ya sa hakan za ta taimaka tare da shiga al’amuran da su ka shafeta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: