Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe kuɗi naira miliyan 854 wajen aurar da zawarawa a jihar.

Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a shafinsa na sa da zumunta a yau Alhamis.

Ya ce za a kashe kuɗin ne wajen aurar da zawarawa a jihar wanda aka zaɓo daga kowacce ƙaramar hukuma ta jihar.

Amincewar na daga cikin abubuwan da su ka tattauna a zaman majalisar zartarwa da aka yi a jihar ranar Laraba.
Tun a baya shugaban hukumar Hisbah a jihar Kano Sheik Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewar, akwai mutanen da su ka nuna sha’awarsu su 1,020.
Auren zawarawa na daga cikin manufofin da gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ayyana yayin yaƙin neman zaɓensa.
An zaɓo mutane 20 daga kowacce ƙaramar hukuma cikin ƙananan hukumomi 44 na jihar, yayin da hukumar Hisbah za ta zaɓo mutane 120 a matsayinta.