Ƙungiyoyin ƙwadago da ma’aikata a Najeriya sun yi watsi da rahoton hukumar ƙididdiga ta fitar a kan ƙarancin marasa aikin yi a Najeriya.

Hukumar ƙididdiga a Najeriya NBS ta fitar da rahoton cewar rashin aikin yi ya ragu da kaso mai yawa a Najeriya la’akari da sabon tsarin da aka fito da shi na aikin yi.
Rahoton ya nuna yadda aka samu masu aiki yi sama da kaso 90 a Najeriya illa kaso kasa da kaso 10 ne kadai ba su da aikin yi a ƙasar.

Wani babba a ƙungiyar ƙwadago ya ce ƙididdigar da su ka bayar na iya rusa nagartarsu a idon mutane a nan gaba.

Duk da cewar ba a sahale masa yin magana ba amma ya shaida cewar ba zai gamsu da yadda aka bayar da sanarwar ba ganin yadda a kowacce rana ake samun mutane da ke barin Najeriya saboda tsananin talauci.
Sakataren ƙungiyar NASU Prince Peter Adeyemi ya ce ya yi mamaki a kan rahoton da hukumar ta fitar duk da cewar ya na gamsuwa da su.
Wanda ya ce a watanni huɗun farkon shekarar da mu ke ciki lokacin ne da ake hada-hadar zaɓe kuma ta yaya za a samu raguwar rashin aikin yi a ƙasar.
Hukumar dai ta ce muddin mutum na yin aikin awa guda a mako to ya na da aiki yi, kuma an fitar da ƙididdigar ne bayan tattara alƙaluman ma’aikatan gwamnati da ƴan aksuwa, masu zaman kansu da manoma.