Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya ce wajibi ne Najeriya ta ci gaba da ɗaukar mataki mai tsauri domin kare martabarta a idon duniya.

Tinubu ya bayyana haka ranar Lahadi a Abuja wanda ya ce za a samar da sauye-sauye masu tsauri a ƙasar domin samun ƙima a wajen sauran ƙasashen duniya.

Bunƙasa ƙasar don ɗaga darajarta na daga cikin dalilan da ya sa za a ɗauki tsauraran sabbin matakan.

Ya ce akwai babban hatsari wajen ƙasar ta ci gaba da biyan bassukan da ake binta da kashi 90 cikin ɗari.

Haka kuma Tinubu ya ce basukan da Najeriya ke bin wasu ƙasashen ba zai ɗore ba.

Sannan za a ɗauki sabbin matakai don ganin an farfaɗo da ƙimar Najeriya a idon sauran ƙasashen.

Shugaba Tinubu ya bayyana haka a wajen taron shekara shekara na ƙungiyar lauyoyin Najeriya wanda aka yi a Abuja ranar Lahadi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: