Shugaban ƙungiyar ‘yan kasuwar man fetur masu zaman kansu reshen jihar Ribas, Joseph Obele, ya roƙi gwamnatin tarayya ta tabbatar da an gyara matatun man da ake afani dashi a cikin gida.

Ya bayyana cewa farashin litar mai wanda aka fi sani da Fetur zai sauko ya dawo ƙasa da Naira 200 kan kowace Lita idan matatun man Najeriya suka ci gaba da aiki.


Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da biyan tallafin man fetur, wanda ya haddasa tashin farashin litar mai da tsadar rayuwa.
Ya ce domin farfaɗo da tattalin arziƙin kasa, shugaba Tinubu ya yi alƙawarin tabbatar da matatar man Patakwal ta fara tace ɗanyen mai a watan Disamba, 2023.
A jiya Juma’a, karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, a ziyarar da ya kai matatar man Fatakwal, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na ganin matatar ta ci gaba da aiki.
Sai dai Obele, a wata hira da ya yi da jaridar Punch a yau Asabar, ya nuna damuwarsa kan yadda karancin dala ke ci gaba da shafar masu shigo da kaya.
Ya kara da cewa farashin fetur zai ci gaba da karuwa idan gwamnati ta kasa lalubo mafita cikin ƙanƙanin lokaci.
