Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamna a jihar Abia ta tsayar da ranar 06/10/2023 domin ya ke hukunci kan ƙararrakin da ke gabanta.

Kotun da ke zaune a Umuahia babban birnin jihar, ta tsayar da ranar domin yanke hukunci kan kalubalantar nasarar gwamnan jihar Alex Otti.
Ɗan takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyar APC a jihar Chief Ikechi Emenike wanda ya ke bukatar nasarar Alex Otti ya bukaci kotun ta rushe nasarar da ya samu.

Ya ce wanda ya samu nasarar bai bayar da takardar fita daaga jam’iyyar ba kafin komaawa jam’iyyar LP.

Sannan sunan Otti ba ya dag acikin jerin sunayen ƴan takarar da aka yi wa rijista kafin ayyanashi a matsayin ɗan takara.
Baayan sauraron kowanne ɓangare a shari’ar kotun ta ayyana ranar 06/10/2023 domin yin hukunci.