Asusun tallafawa kananan yara a majalissar dinkin Duniya UNICEF ya ce, kimanin kananan yara miliyan 333 ne su ke rayuwa cikin matsanancin talauci a fadin duniya.

Rahoton daga UNICEF da bankin duniya ya nuna cewa, annobar cutar sarkewar numfashi ta CORONA ta zamto sanadiyyar raguwar matsanancin talauci ga kananan yara miliyan 30 kasa da yadda aka yi hasashe a baya.
Bisa la’akari da kiddigar masana, duk yaro 1 cikin yara 6 a duniya, yana rayuwa ne kasa da Dala 2 da rabi a rana.

Babbar daraktar UNICEF Catherine Russell a jiya Laraba ta bayyana cewa, matsaltsalun da suka hadar da annobar CORONA, rikici, sauyin yanayi da durkushewar tattalin arziki sun kawo cikas ga cigaban da ake samu. Sun jefa miliyoyin kananan yara cikin matsanancin talauci.

A nasa bangaren, babban daraktan bankin duniya akan fatara da daidaito Luis-Felipe Lopez-Calba, ya bayyana lamarin a matasayin abinda ba za a lamunta ba.
Lopez ya ce, a duniyar da yara Miliyan 333 suke rayuwa cikin matsanancin talauci, za a samu ba iya tauyewar abubuwan bukata ba, har da kima, buri da kuma damarmaki.
Rahoton kuma ya nuna, kashi 40 cikin 100 a yankin saharar Afirka suna cikin matsananciyar fatara, kuma shi ne kason da ya fi muni fiye da ko ina a duniya.