Majalissar wakilan Najeriya ta bayyana cewa ba za ta amince a mikawa ƙasar Kamaru wani gari a jihar Adamawa ba.

Majalissar ta bayyana haka ne ta bakin shugabar kwamitin dake Kula da yankuna Beni Lar ga yan jarida.
Lar ta ce majalisa ba ta amince da a bai wa kasar kamaru yanki Sina ba dake da iyaka da kasar ta Kamaru ba.

Ta ci gaba da cewa kamar yadda aka bukata a bai wa kamaru yankin na Sina ba zai yuwu ba saboda yankin yana cikin kasa Najeriya ba a kan iyaka yake ba.

Ta ci gaba da cewa za su shiga jihar Adamawa domin kara bincike akan yankin na Sina kuma tuni aka sanarwa da gwamnatin jihar.
Wani masani a yanki ya bayyana cewa yankin Sina ba a kan iyaka yake ba yana cikin kasa Najeriya Kuma kotun Duniya TCJ ce ta raba yankin.