Rundunar sojin kasa Najeriya ta bayyana cewa ta hallaka akalla yan ta’adda 151 a fadin kasa Najeriya.

Rundunar Operation hadin Kai sun Kama akalla yan ta’adda 456 a cikin makonni biyu a yankuna daban-daban.
Mai magana da yawun hukumar sojin na kasa mista Eward Buba ne ya bayyana haka a yau Alhamis.

Ya ce nasarar ta Samu ne bayan da sojin suka kai hare hare a yankuna yan ta’addan.

Ya ce sun yi nasarar hallaka yan bindigan 151 da Kuma kama 456 wadanda suke hannu.
Sannan su yi nasarar kwace bindigu na gida da na waje da kuma wukake.
Kuma akwai harsashai masu tarin yawa da mashina da motoci da sauran kayayyakin amfani.