Akalla majami’un bautar kiristoci kimanin 200 ne aka rufe sakamakon hare-haren yan bindiga a jihar Kaduna.

Wannan sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa reshen jihar Kaduna Jhon Rev Dayab.

Jhon ya ce akalla an hallaka limamin coci 23 a jihar ta Kaduna.

Kuma hakan ya faru ne sakamakon yan bindiga da suka dinga kai hari a cikin shekaru Hudu da suka gabata.

Jihar Kaduna na cikin jihohin da ke fama da matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.

Sai dai ko da yaushe gwamnatin tarayyar da ta jiha suna bayyana cewa za a magance matsalar tsaron kasar baki ɗaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: