Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Jamila Bio Ibrahim a matsayin minister matasa, yanzu tana jiran tantancewa ne kawai daga majalissar dattawa.

Haka zalika shugaba Tinubun ya kuma amince da nadin Ayodele Olawande a matsayin karamin ministan matasan, shi ma yana jiran tantancewa ne kawai daga majalissar dattawan tarayyar Najeriya.

Jamila dai matashiyar likita ce wacce kwanannan ta kasance shugabar kungiyar mata matasa ta PYWF. Sannan kuma ta rike babbar mai taimakawa ta musamman ga gwamnan jihar kwara a kan cimma muradun karni.

Olawande kwararren masanin hanyar ci gaban al’umma ne, kuma ya rike shugabancin matasan jam’iyya mai mulki ta APC, a kwanannan ya yi aiki a ofishin mai taimakawa shugaban kasa na musamman akan bijiro da sabon tsari daga shekarar 2019 zuwa shekarar 2023.

Shugaban kasa Tinubun ya hori sabbin ministocin da su kasance sun nuna kwazonsu, fikirarsu, da samar da abu mai kyau kamar yadda aka san matasan Najeriya su na yi lokacin gudanar da ayyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: