Shugaban kasa Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya isa kasar Amurka a jiya Lahadi, don halartar babban taron majalissar dinkin duniya karo na 78.

Wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa, Tinubu ya sauka a babban filin kasa da kasa na sauka da tashin jiragen sama na JF Kennedy a birnin Niyok da misalin karfe 6 da mintuna 45 na yammaci.
Shugaban yana jagorantar tawagar wakilan Najeriya dan halartar babban taron, wanda za a fara daga 18 zuwa 26 ga watan Satumba.

Shugaba Tinubu ya samu tarba daga ministan harkokin wajen Najeriya Yusuf Tuggar, babban wakilin Najeriya a majalissar dinkin duniya Tijjani Muhammad Bande da sauransu.

Sai dai NAN ta ruwaito cewa yanayin karbar da aka yi wa shugaban ya sha bam-bam da wanda aka saba gani, yanda ake hawa dogon layi don shugaban kasa.
Wannan karon manyan jami’ai uku ne kacal a filin sauka da tashin jiragen don tarbarsa, sai sauran manyan jami’an Najeriya da su ka tsaya a Otal din Millennium Hilton don tarbarsa.
A cikinsu akwai ambasadojin Najeriya a Amurka, da gwamnonin Najeriya a jihohin Akwa Ibom, Oyo, Kaduna, Gwambe, Kwara da sauransu.