‘Yan sanda a Jigawa sun samu nasarar daƙile wani hari da aka yi yunƙurin garkuwa da wani tare da kama makamai.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar DSP Lawal Shiisu Adam ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai tare da aikewa da Matashiya TV.

Lawal Shiisu ya ce sun kuɓutar da wani Ahmad Abdullahi wanda ƴan bindigan su ka harbeshi, da kuma wani Isyaku Umar mai shekaru 37 a duniya wanda aka yi yunƙurin garkuwa da shi.

Sai dai ya na asibitin koyarwa na Dutse don cigaba da kula da lafiyarsa.

Hakan ta faru a ranar Lahadi da daddare, yayin da ƴan bindigan su ka tare hanyar Kwanar Garki a ƙaramar hukumar Babura a jihar Jigawa.

Sai dai sun yi rashin sa’ar kama waɗanda su ka yi yunƙurin garkuwa da mutumin, bayan da su ka bar motarsu ƙirar Vectra su ka gudu.

A cikin motar ƴan sandan sun ga bindiga ƙirar AK47, da harsashi guda 15.

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya jinjinawa jami’ansa tare da bayar da umrni don ganin an kama waɗanda su ka gudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: