Babban kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ta Najeriya TCN ta bayyana daukewar hasken lantarki a fadin Najeriya karo na biyu cikin mako guda.

 

Hukumar samar da wutar ta bayyana cewa kimanin Megawat 3, 594.60 ne ya sake sauk a yau Talata.

 

Ko da a satin da ya gabata ma, an tsinci kai a cikin duhu a fadin kasar wanda ya haifar da duhu da tsayawar alamura na tsawon awanni 12.

 

Hukumar rarraba wutar lantarki ta kasa TCN ta bayyana makasudin faruwar hakan kan matsalar da babbar tashar wutar lantarki ta Osogbo da ke jihar Osun ta samu.

 

Ko da ranar Alhamis da ta gabata, kafin afkuwar wannan al’amari a yau ministan Adebayo Adelabu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne sakamakon matsalar da babbar ma’adanar wutar ta kainji ta haifar.

 

Sannan ministan ya bayyana shawo kan al’amarin nan ba da jimawa ba.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: