Ƙasar Amurka ta gargaɗi ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su kiyaye wajen ziyartar wasu jihohi da ka iya faɗawa cikin hatsari.

Sanarwar na zuwa ne bayan gudanar da wani bincike da su ka gano an samu ƙaruwar aikata manyan laifuka a jihohin.
Jihohin sun haɗa da Borno, Adamawa, Yobe, Kogi, Bauchi, Kaduna, Kano, Gombe, Bayelsa, Rivers, Enugu da jihar Bayelsa.

Sauran jihohin su ne Imo, SokOto, Zamfara, Katsina, da jihar Abia.

Ƙasar ta gargaɗi mutanenta da su kiyaye wajen ziyartar waɗannan jihohi domin su na iya faɗawa cikin tarkon masu garkuwa da mutane ko wasu miyagun laifuka.
Binciken da su ka yi sun gano cewar masu satar mutane domin neman kuɗin fansa na amfani da ƙarin mutane a wasu sassa domin cimma muradinsu.
Sannan gwamnatin Amurukan ta buƙaci ƴan ƙasar mazauna Najeriya da su ƙara sanya idanu a kan dukkanin zirga-zirgarsu don gudun faɗawa hatsari.
