Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce kimanin mutane dubu huɗu ne a gidan ajiya da gyaran hali sanadin gaza biyan tara a kotuna.

Ministan harkokin cikin gida Olubinmi Tunji Ojo ne ya bayyana haka bayan tabbatar da alƙaluman.
A wata sanarwa da masharwacin ministan a kan kafofin yaɗa labarai Alao Babatunde ya sanyawa hannu a yau, ya ce kashi 70% cikin ɗari na mutanen da su ke gidan yari na jiran hukunci.

Ministan ya ce Najeriya na iya ƙoƙarinta don ganin ta magance matsalolin da ke gabanta musamman na aikata laifuka.

Sau da yawa, ana samun gwamnoni da ke yafewa mutane mazauna gidan gyaran hali domin rage cunkuso a ciki.
