Wasu da ake zargin yan ta’adda ne sun kone gidan Dan majalisa Mai wakilatar Orlu ta jihar Imo.

 

Kamar yadda yan ta’addan suka wallafa a wani faifan bidiyo an hangi yadda suka kone gidan Dan majalisa a jihar ta Imo a jiya juma a.

 

Da yake zantawa da manema labarai Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar Imo ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Ya ce lamarin ya faru ne a karamar hukumar Orlu ta gabas a yankin Abara ta jihar Imo.

 

Ya ci gaba da cewa yan bindigan sun isa gidan Dan majalisa mai suna Conice wanda akafi sani da Omeoga da daddare.

 

Sannan sun kona gidan tare da diban kayan amfani.

 

ya ce lokacin da suka isa gidan dan majalisa baya gida bayan zuwan su da Mayan makamai.

 

Sai dai rundunar yan sandan jihar Imo ta ce tana cigaba da bincike akan lamarin Kuma za a Kama wadanda ake zargi akan lamarin nan ba da jimawa ba.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: