Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya, da su ci gaba da jure halin matsin rayuwa da aka shiga dalilin janye tallafin man fetur.

A jawabinsa na ranar murnar cikar Najeriya shekaru 63 da samun ‘yancin kai, yace an shiga halin kuncin ne biyo bayan janye tallafin man fetur.

“Ina sane da halin kuncin da ya zo, ina da zuciyar ji da kuma idanun gani, kuma ina da burin sanar da ku dalilin da zai sa mu jure wannan yanayin na matsin rayuwa,” Tinubun ya ce.

Ya kara da cewa “kawo sauyi Abu ne mai da zai iya zama mai ciwo, amman kuma shi ne nagartaccen abin da muke bukata a nan gaba.”

“Ban so mu kasance a cikin wannan halin matsin rayuwa da muke ciki ba a yanzu, amman dole sai mun jure shi domin kyautatuwar goben mu.”

Shugaba Tinubun dai ya sanar da janye tallafin man fetur ranar 29 ga watan Mayun da ya gabata, a jawabinsa na ranar karbar rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya.

Tun daga wancan lokacin farashin man na fetur ya ninka kudin sa har kusan sau uku a manyan biranen Najeriya, daga kasa da Naira 200 zuwa kusan Naira 600 a kowacce lita.

Tashin farashin man ne kuma ya janyo sanadiyyar gagarumin hauhawar farashin kayayyakin amfanin yau da kullum, da janyo tabarbarwar tattalin arzikin miliyoyin ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: