Sama da mutane 563 da ke Unguwar Tana’a cikin karamar hukumar Yola ta gabas a Jihar Adamawa ambaliyar ruwan ta raba da muhallansu a Jihar.

 

Mataimakin gwamnan Jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, bayan ziyarar jaje da ya kaiwa al’ummar yankin a ranar Laraba.

 

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa gwamnan Jihar yayi alkawari za a kawo masu dauki domin rage masu radadin halin da suka shiga a yayin ambaliyar ruwan.

 

Bayan faruwar lamarin mutanen da abin ya shafa sun samu mafaka a makarantar Sakandare GDS da ke yankin Limawa Jimeta da ke Yola babban birnin Jihar.

 

Shugaban makarantar Musa Hassan Jada ya bayyana cewa mutanen da abin ya shafa sun tare ne a ajujuwa bakwai da ke cikin Makarantar.

 

Amabilayar ruwan ta faru ne dai bayan cikar da kogin Benue ya yi, bayan yin mamakon ruwan sama, tare kuma da sako ruwan Dam na Lagdo da ke Kasar Kamaru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: