Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina sun tabbatar da kama wani da ake zargin ya na da hannu a yin garkuwa da daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya ta FUDMA da ke Dutsan-Ma a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar ASP Abubakar Aliyu ne ya tabbatar da kama wanda ake zargin.


Kakakin ya ce rundunar ta kama wanda ake zargin ne da bai wa ‘yan bindigan bayanan sirri da su ka kama daliban.
Aliyu ya kara da cewa ya zuwa yanzu jami’ansu sun bazama cikin dazukan da ke Jihar domin kuɓutar da dalibai matan biyar da aka yi garkuwa dasu a dakunan kwanansu da Jami’ar.
Kakakin ya bayyana cewa za su ci gaba da gudanar da bincike akan mutumin domin samun wasu bayanai daga gareshi.
Masu garkuwar sun yi garkuwa da daliban ne a ranar Laraba ne 4 ga watan Oktoban da muke ciki, a ɗakunan kwanansu da ke cikin jami’ar.