Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce, zai ajiye makaman yaki da nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne kawai idan har kotun koli ta tabbatar da nasararsa.

Atiku ya yi wannan jawabin ne a wajen wani taron manema labarai da ya gudanar a yau Alhamis, a birnin tarayya Abuja.

Ya yi taron manema labaran ne dai, don ya yi musu jawabi dangane da kundin bayanan karatun shugaba Bola Tinubu, wanda jami’ar Chicago da ke kasar Amurka ta saki.

Lokacin da ‘yan jaridu su ka yi masa tambaya cewa, shin ko zai dakata da yakin shari’ar da yake yi dangane da nasarar Bola Ahmed Tinubu?

Atiku ya ce “har yanzu lamarin yana gaban kotu, kuma zan dakata ne kawai idan kotun ta yi hukunci. Idan kotun ta bani nasara shikenan, idan kuma kotun ta bai wa Tinubu nasara ma shikenan. Babu wata kotun ta sama da ta koli, nan ne karshen tikewa.”

Sannan kuma Atikun ya karyata zarge-zargen da ake cewa ya ci amanar Bola Tinubun, wadanda mutane suke kallo a matsayin tsohon abokin siyasarsa.

Atikun ya ce “Ban yarda da Tinubu ba, eh haka ne mun yi tafiya tare a shekarar 2007. A birnin Legas lokacin babban taron jam’iyya, na samu nasara kuma na karbi tikitin tsayawa takara a jam’iyya. bayan na yi nasara, ya turomin manyan ‘yan jam’iyya kusan mutum 5 ko 6, sun same ni sun gaya min cewa Bola Tinubu yana son ya zama mataimaki na.

“Sai na ce musu dukkan ku dattijai ne, me Ku ke gani idan har aka yi takarar Musulmi da Musulmi a takarar shugaba da mataimaki ? Su ka amsa gaba dayansu cewa basa goyon baya.

“Sai na ce to su je su Sanar da shi, wannan ce karshen alakar siyasarmu. Shikenan ya tafi ya goyi bayan Umaru Musa ‘Yar Adua. Menene abin cin amana a nan? “

Leave a Reply

%d bloggers like this: