Hukumar tsaron fararen hula a Najeriya NSCDC sun kama mutane 11 da ake zargi da satar kayan gwamnati.

 

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar na Abuja Comfort Okomanyi ya fitar yau Laraba.

 

Yayin holen wadanda ake zargi yau a harabar hukumar, kwamandan hukumar ya lashi takobin magamce dukkannin barna a Abuja.

 

Ya ce mutane 11 da aka kama akwai masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba.

 

Sannan kwamandan ya ce zai tabbatar hukumar ta sake zage damtse wajen kare kadarorin gwamnati a Abuja.

 

Ko a baya bayan nan sai da hukumar ta kama easu mutane da ke satar kadarorin gwamnati a Abuja.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: